1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashin hankali a Iraƙi

May 15, 2010

Hukumar zaɓen Iraƙi ta kawar da zargin maguɗi, a dai dai lokacin da ƙasar ke fiskantar sabbin tashe tashen hankula

https://p.dw.com/p/NOf3
Tashin bam a IraƙiHoto: AP

Hukumar zaɓen ƙasar Iraƙi ta ce babu wata shaidar dake nuni da yin aringizon ƙuri'u a zaɓen 'yan majalisar dokokin ƙasar da ya gabata. Hukumar ta bayyana hakanne bayan da ta kusan kammala sake ƙirga ƙuri'un da aka kaɗa. A tsakiyar watan Afrilu hukumar ta ba da umarnin sake ƙidayar ƙuri'un biyo bayan buƙatar Firimiyan ƙasar Nuri Al-Maliki wanda ya yi zargin tabka maguɗin zaɓe bayan da ya kasa samun nasara. A wani labarin kuma mutane 25 suka mutu wasu da dama suka jikkata, lokacin da aka kai wasu tagwayen hare haren bam a wani filin wasan ƙwallon ƙafa a arewacin ƙasar ta Iraƙi. Waɗanda suka shaida abin da ya faru sun ce mutane kimanin 250 ke kallon wasan lokacin da maharan suka far musu kuma babu ɗan sanda ko wani jami'in tsaro dake wurin. Kana an kai wani hari kusa da masallacin 'yan Shi'a, inda a nan ma mutane da yawa suka mutu wasu suka ji rauni. Wannan watan dai shi ne aka fi samun tashin hankali a Iraƙi, tun farkon wannan shekara.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Mohammed Nasiru Awal