1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashin hankali ya ɓarke a Filipins

Halimatu AbbasAugust 23, 2010

Wani tsohon ɗan sanda ya yi garkuwa da 'yan yawon buɗe ido a Filipins

https://p.dw.com/p/OuHQ
Bus ɗin da ke ɗauke da 'yan yawon buɗe ido a Manila.Hoto: AP

Wani tsohon kaftin ɗin 'yan sanda da ya yi garkuwa da wasu masu yawon buɗe idanu a birnin Manila na ƙasar Filipins ya kashe akasarin fasinjojin da yayi garkuwa da su. Tsohon ɗan sandan wanda ke ƙorafin an sallame shi daga aiki ba bisa ƙa'ida ba, tun da farko ya sheda wa wani gidan radiyo cewar ya kashe wasu daga cikin fasinjojin motar bus ɗin.'Yan sanda ɗauke da makamai ne dai suka yi wa motar bus ɗin ƙawanya da zummar ceto fasinjojin. Sai dai kamar yadda tashoshin talabijan da dama yanzu haka ke nuna wannan ɗauki-ba-daɗin tsakanin jami'an tsaron da tsohon ɗan ɗan sandan, akwai dai 'yan yawon buɗe ido 25 a cikin wannan bus, kafin daga bisani ya saki wasu da suka haɗa da yara ƙanana uku. Akasarin 'yan yawon buɗe idon dai 'yan ƙasar China ne.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Halima Balaraba Abbas