1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tashin nakiyoyi a birnin Colombo

Zainab A MohammedAugust 14, 2006
https://p.dw.com/p/Bu5w

Kimanin mutane 7 ne suka rasa rayukansu kana wasu 17 suka jikkata,a tashin wasu sinadrai masu nasaba da bomb a fadar gwamnatin Sri lanka dake Colombo.Gwamnatin Sri lankan ta danganta wannan hatsari da nakiyar karkashin kasa, da yan tawayen kungiyar Tamil Tigers suka dasa da nufin haran ayarin motocin babban jamiin jakadancin pakistan.Tashin wadannan nakiyoyi ya auku ne saoi kalilan ,da fitar da wata sanarwa dake gargadin dakarun gwamnati dasu dakatar da harin da suke kaiwa yan kungiyar ta Tamil Tigers.Tun da farko dai yan tawayen sun zargi gwamnati da kai harin boma bomai a wata cibiyar yara marayu dake yankinsu,harin daya kashe yaran makaranta mata 61.Gwamnati kasar dai ta karyata wannan zargi,dacewa dakarunta sun kai hari cibiyar hirarwar yan tamil tigers din.Kididdiga na nuni dacewa,cikin tsukin makonni 3 da fada ya barke tsakanin bangarorin biyu,kimanin mutane sama da dubu 100 ne,suka rasa matsugunnensu.