Tashin zaune tsaye a iraqi
February 22, 2006Shugaban mabiya darikar shi´a a Iraq, Ayatollah Ali Al sistani ya bukaci magoya bayan sa dasu kasance masu bin doka da oda.
Wannan kira dai yazo ne bayan da dubbannin mabiya darikar shi´a a Iraq suka hau kann titunan garin Samarra suna gudanar da zanga zangar nuna fushin su ga wani hari da aka kai izuwa cibiyar ibada mafi girma ga yan shi´a a kasar.
Rahotanni dai sun nunar da cewa harin na bama baman ya haifar da lalata wani bangare na ginin masallacin na yan shi´a..
Ya zuwa yanzu dai jami´an yan sanda a kasar sun shaidar da cewa mabiya darikar ta shi´a sun kai hare hare iri daban daban ga masallatai na yan Sunni a kalla 60 a wannan rana ta laraba.
Tuni dai Faraministan kasar Ibrahim Al Jafari ya bayar da hutun kwanaki uku na zaman makoki, a sakamakon faruwar wannan abu, daya ke kokarin sake haifar da zaune tsaye a kasar.