1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin Faransa a rashin cigaban Haiti

January 30, 2010

Irin rawa da Faransa ta taka a tarihin Haiti, bayan samun 'yancin kai a 1804

https://p.dw.com/p/LnhY
Shugaba Rene Preval na HaitiHoto: AP

A shekara ta 1994 ne Dakarun Amurka suka cimma nasarar kawo karshen mulkin kama karya na sojoji a kasar Haiti. Sai dai duk dacewar tana samun agaji daga ƙasashen Duniya sakamakon bala'in data tsinci kanta a ciki na girgizar kasa, akwai alamun cewar da sauran tafiya a farfado da wannan tsibirin daya kasance a karkashin Mulkiin mallakan faransa sama da shekaru 100 da suka gabata.

Kafin shekaru 200 da suka gabata dai, tsibirin Haiti ya kasance a karkashin mulkin mallakan kasar Faransa. A wancen lokacin dai Tsibirin na samun ingantuwar kuɗaden shiga, sakamakon albarkatun sukari da Allah ya huwacewa Haiti, wanda kuma ya sa ta kasance ta farko a jerin kasashen dake fitar da sukari zuwa kasuwannin Duniya,duk da matsin lamba daga ɓangaren shugabannin mulkin mallaka na Faransa.

A saboda samun araha dai ,Faransawan kanyi anfani da bayi 'yan Afrika a gonakin raken. Kimanin bayi dubu 800 ne ke aiki a yanayi mawuyaci a gonakin rake da kofi.Da yawa daga cikin su na mutuwa da wuri saboda tsananin wahala, kuma domin tabbatar da ɗorewan aiki, Faransan na kai bayi kimanin dubu 50 a kowace shekara zuwa Haiti.

Haiti Erdbeben Blauhelme aus Brasilien in Port-au-Prince
Sojin MDDHoto: AP

sai dai an samu sauyin lamura da juyin juya hali a Faransa. Saboda a dalilin neman 'yanci da daidaituwa ne suka gudanar da tarzomar data bawa Haitin 'yancin cin kanshin kanta a shekarata 1804. Hakan kuwa ya jagoranci Faransan kakabawa Tsibirin takunkumin tattalin arziki.

A shekara ta 1825 ne Faransa ta nemi ta fara karɓan kudaden diyya na kimanin Franc miliyan 150, kasancewar a yanzu bata cin moriyar albarkatun tsibirin na Haiti.

Tsawon shekaru bayan samun 'yanci dai Haitin ta cigaba da biyan makuddan kuɗaɗe a matsayin diyya wa uwargijiyarta Faransa, batu da manazarta suka danganta da jefa ta cikin halin rashin cigaba duk da kasancewarta kasa ta farko a latin Amuriak data samu 'yancin kai.

Tun daga ranar 1 ga watan janairun 2004 ne aka girke rundunar sojin sama da 7,000 da ake kira MNUSTAH a haiti amma har yanzu da sauran tafiya inji kakakin rundunar David Wimhurst..

"Ya ce Kusan shekaru biyar kenan da kasancewarmu a nan,kuma zaman lafiya na nufin tabbatar da doka da oda a Haiti. Ma'ana samarda da Yansanda da zasuyi aikin tsaro a kasar.,tare da tabbatar kare hakkin jama'a, da kafa dokar da zata tabbatar da adalci da gaskiya a bangaren shari'a.Kazalika da ingantaccen tsaro a kan iyakokin ruwa da hanyoyi.Waɗannan sune muhimman abubuwa da zamu tabbatar."

Haiti Flash-Galerie Raboteau Haiti
Port au princeHoto: Rottscheidt

Wata matsala babba kuwa itace, a yanzu haka Haitin ce ke bukatar tallafi daga kasashen Duniya, amma kusan ana iya cewar babu wata gajiya da zaa iya samu daga gareta.Kamar yadda wani kwararre daga wata cibiyar bada agaji ta latinamurka, Michael Huhn ya yi nuni....

"Ya ce na taba fadawa wani dan kasar Haiti cewar,idan ruwa ya ciye Haiti, zai zame babban damuwa wa jama'ar kasar,amma hakan bashi da wani tasiri ga Duniya"

A yanzu haka sakamakon wannan bala'in girgizar kasar da Haitin ta tsinci kanta ciki ya sanya kasar Faransan yafe mata sauran basussukan da take binta.

Mawallafiya: Zainab Mohammed

Edita : Abdullahi Tanko Bala