1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin janyewar dakarun Amirka daga Iraƙi.

Halimatu AbbasAugust 19, 2010

Ana ci gaba da nuna damuwa da janyewar dakarun Amirka daga Iraƙi.

https://p.dw.com/p/Ort6
Janyewar sojojin Amirka daga Iraƙi.Hoto: AP

Da yawa daga cikin al'umar Iraƙi sun bayyanar da fargabansu game da taɓarɓarewar al'amuran tsaro da kuma rashin kwanciyar hankali bayan janyewar dakarun Amirka daga wannan ƙasa.

A lokacin da a ɓangare ɗaya wasu 'yan ƙasar Iraƙi ke bayyana jin daɗinsu game da janyewar dakarun Amirka da suke wa kallon 'yan mamaya dubi ga alƙalumma da ke nuni da cewa dubun dubatan 'yan ƙasar ne suka rasa rayukansu tun sanda sojojin na Amirka suka ƙaddamar da yaƙi a ƙasar a shekarar 2003, kuma da wuya a samu iyalin da wannan yaƙi bai shafa ba. A ɗayan bangaren kuwa wasu

bayyana damuwarsu suka yi cewa za a samu ƙaruwar rincaɓewar halin tsaro da kuma hare-haren ta'addanci ko kuma sake ɓarkewar rikice-rikice tsakanin rukunonin al'uma da 'yan bindiga.

Deutsche Welle ta gudanar da bincike a birnin Bagadaza inda da yawa daga cikin al'uma suka bayyana tsoronsu da kuma shakkunsu. Ga dai abin da wasu ke cewa:

"Muna fama da matsalar taɓarɓarewar halin tsaro . Akwai haɗarin fuskantar hare-hare saboda haka mace ba ta iya fita ba tare da cewa mahaifinta ko ɗan uwanta ko kuma mijinta yayi mata rakiya ba."

"Komai ya sukukuce a ƙasar nan. Ga rashin gwamnati ga kuma taɓarɓarewar halin tsaro."

Irak Al-Kaida-Video zeigt Kindersoldaten im Irak
Mayaƙan Al-Ƙai'daHoto: AP

A haƙiƙa an fuskanci ƙaruwar hare-haren 'yan al-Ƙa'ida musannan ma akan 'yan sanda da sojoji . A ma shekaran jiya Talata sai da aka aiwatar da ire iren waɗannan hare-hare da suka yi sanadiyar mutuwar masu neman shiga aikin soja guda 59. Ba ma daga 'yan al-Ƙa'ida ne kaɗai ake fuskantar barazana ba. Ana fuskantar ƙaruwar taɓarɓarewar halin tsaro a ƙasar ta Iraƙi ne sakamakon rashin takamammiyar gwamnatin tun kusan watanni shida da suka gabata. An dai yi ƙoƙarin kafa gwamnatin haɗaka ta jam'iyyar Eyad Alawi da ta lashe zaɓe da gwamnatin wucin gadi ta Nuri Al-Maliki da kuma ƙawancen Kurdawa na arewacin ƙasar amma ba tare da samun nasara ba- inda hakan ya sa masu matsanancin ra'ayi na addini da 'yan ta'adda ke amfani da wannan giɓi suna aika-aikarsu a ƙasar ta Iraƙi da ma maƙwabciyarta Iran da ke da dangantakar kut da kut da ita .

Irak USA General Raymond Odierno Fotomontage Bombenanschlag in Bagdad
Janar Raymond Odierno, komandan rundunar Amirka a Iraƙi.Hoto: AP/DW Fotomontage

A cikin wata fira da CNN ta yi da shi tun wasu watanni da suka gabata komamndan dakarun Amirka, General Raymonnd Odierno ya bayyana tsoron sake ɓarkewar tashe -ashen hankula inda yake cewa:

"Za mu ci gaba da zama a nan ƙasar . Ba zamu janye baki ɗaya daga wannan ƙasa ba saboda cewa wajibi ne mu kare al'umar Iraƙi".

To sai dai har yanzu tana ƙasa tana dabo kamar yaddda ya bayyanar a cikin wata fira da aka yi da shi a baya-bayan nan inda ya ce har yanzu ana fama da rikici tsakanin Larabawa da Kurdawa, akan yankin Kirkuk mai arziƙin man fetur. Hakazalika a 'yan makonnin da suka gabata sai da takwaransa a ƙasar ta Iraƙi, Babekar Sebari ya yi kashedi da cewa dakarun sojin ƙasar ba su samu horon da ya kamata ba. A ma cikin firarraki da dama da aka yi da shi yayi kira da a bar dakarun Amirka a ƙasar ta Iraƙi har ya zuwa shekarar 2020.

Mawallafiya/Edita: Halima Balaraba Abbas