1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afirka A Jaridun Jamus

May 15, 2009

Yadda ƙungiyar tattalin arziƙi da raya ƙasa ta OECD ta bayyana makomar tattalin arziƙin Afurka a ƙarƙashin rikicin kuɗi na duniya.

https://p.dw.com/p/HrKa
Tambarin ƙungiyar OECDHoto: imageshop/DW


A wannan makon dai rahoton da ƙungiyar tattalin arziƙi da raya ƙasa ta OECD ta bayar dangane da makomar tattalin arziƙin Afurka a ƙarƙashin yanayin rikicin kuɗin da ake fama da shi a duniya shi ne ya fi ɗaukar hankalin masharhanta na jaridu da mujallun Jamus, ko da yake sun taɓo sauran batutuwan dake ci gaba da addabar wannan nahiya ba ƙaƙƙautawa, kamar dai sabon halin da aka shiga a ƙasar Somaliya, inda jaridar Berliner Zeitung ke cewar:


"Ɗaruruwan mutane suka tsere daga Mogadishu, babban birnin ƙasar Somaliya, sakamakon mummunar arangamar da ta sake kunno kai kwanakin baya-bayan nan. A halin da ake ciki yanzu haka ba wanda ya san ranar da rikicin ƙasar ɗan shekaru 18 zai kawo ƙarshensa, saboda ga alamu dakarun ƙungiyoyin fafutukar kafa shari'ar musulunci sun ƙara ƙarfafa ɗamarar makamansu don shiga arangama ta dogon lokaci da abokan gabarsu dake rufa wa gwamnatin wucin gadi ta Sheikh Sharif Ahmad baya, wanda shi kansa tsofon ɗan fafutukar kafa shari'ar ta Musulunci ne a ƙasar Somaliya."


A wannan makon ne ƙungiyar tattalin arzƙi da raya ƙasa da OECD ta gabatar da rahotonta a game da tattalin arziƙin Afurka tana mai ba da la'akari da tasirin da rikicin kuɗin da ake fama da shi zai yi akan tattalin arzƙin ƙasashen nahiyar. A lokacin da take tofa albarkacin bakinta akan haka jaridar Süddeutsche Zeitung cewa tayi:


"A gaskiya dai ba taɓarɓarewar tattalin arzƙin duniya ne kawai ummal'aba'isin matsalolin Afurka ba. Domin kuwa su kansu shuagabannin ƙasashen nahiyar sun daɗe suna wa al'amuran ƙasashensu riƙon sakainar kashi, a yayinda su kuma kamfanonin ƙetare dake zuba jari a ƙasashen suka sa ido suna kallon abin dake faruwa ba tare da sun yi katsalandan ba. Galibi ma dai su kansu waɗannan kamfanoni suna da rabonsu na alhakin abubuwan dake faruwa, inda suke kame bakinsu ko kuma ma su shiga ba da cin hanci da rashawa da daɗaɗa wa masu riƙe da madafun iko saboda neman alfarma."


Ita kuwa jaridar kasuwanci ta Handelsblatt cewa tayi:


"Ko da yake rikicin kuɗin da ake fama da shi a sassa daban-daban na duniya zai shafi Afurka, amma na ɗan gajeren lokaci, musamman ma ganin cewar babu wani canjin da aka samu dangane da yawan jarin da China ke zubawa da kuma taimakon raya ƙasar da ake ba wa kasashen nahiyar. Ƙwararrun masana na ƙungiyar tattalin arziki da raya ƙasa ta OECD sun yi hasashen cewar nan da nan ƙasashen na Afurka zasu sake farfaɗowa daga raɗaɗin rikicin inda a shekara mai zuwa ake sa ran cewar ƙasashen zasu samu bunƙasar kashi 4,5 cikin ɗari ga tattalin arziƙinsu, musamman ma ƙasashen dake ɗaukar matakan garambawul ga tattalin arziƙinsu a nahiyar ta Afurka."

Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal

Edita: Abba Bashir