1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin wasan barkwanci ga rayuwar al'umma

March 28, 2017

Daf da lokacin da aka yi bikin tunawa da ranar da aka ware ta musammun ta wasan barkwanci a duniya a Nijar wasan wanda ya taka rawa wajen hadan kan al'umma a yanzu yana ja da baya saboda rashin tallafi.

https://p.dw.com/p/2a8Vz
Ministan al'adu na Nijar Assoumana Malam Issa
Ministan al'adu na Nijar Assoumana Malam IssaHoto: DW/A. Adamou

 A Jamuhuriyar Nijar daf da lokacin bikin ranar da aka ware ta musammun saboda wasan kwaikwayo a duniya,'yan wasan barkwancin na Damagaram inda nan ne tushen wasan sun koka game da irin yada sha'anin wasannin ke ja da baya, shekara da shekaru saboda rashin tallafi da ba sa samu daga masu hannu da shuni da kuma gwamnati.Wasan barkwancin dai wani abu ne da ke taimaka wa wajen gyara hallayar dan Adam game da irin yanayin da ya samu kansa a ciki.Tsofin gwamnatocin mulkin kama karya a Nijar sun rika yin amfani da wasan barkwanci domin fadikar da al'umma a game da tsaron kasa da samar da zaman lafiya a tsakanin al'umma, har ma da shugabannin na yanzu su kan yin amfani da wasannin barkwancin da hada kawunan al'ummar kasar.