1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tasirin zaben Macron ga matasan Najeriya

May 18, 2017

Zaben matashi mai jini a jika a matsayin sabon shugaban kasar Faransa, ya zaburar da kungiyoyin matasa da dama a Najeriya, wajen ganin sun yi wani yunkuri na kawo sauyi a siyasar kasarsu.

https://p.dw.com/p/2dCVv
Sabon shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron
Sabon shugaban kasar Faransa Emmanuel MacronHoto: Getty Images/AFP/F. Mori

Babu shakka zaben na Emmanuel Macron a matsayin sabon shubanan kasar Faransa wanda kuma ke da kimanin shekaru 39 a duniya da ya sanya ya kasance matashi na farko a kasar da ke da karancin shekaru wajen jagorancin kasar, ya bai wa matasan daukacin kasashen Afrika mamaki da sha'awa. Wannan lamari ne ya sanya matasa a Najeriya yunkuri na fara shiri tun daga yanzu na yin tunanin neman kujerun shugabancin kasarsu.  Matasan dai na ganin lokaci ya yi da za su tashi tsaye domin sauya akalar siyasar kasar, da tsofaffi suka mamaye kana suka kasance wadanda ke shugabanncin kasar na tsahon lokaci, ba tare da sun ba wa sababbin jini damar taka tasu rawar a harkokin mulkin demokuradiyya ba. Mallam Badaru Balarabe Birnin yaro shi ne shugaban matasa 'yan siyasa a jihohin arewacin Najeriya, ya kuma bayyana cewa nasarar ta Macron nasara ce ta matasa baki daya, kasancewar nasarar tasa ta zaburar da matasa musamman ma a nahiyar Afirka na ganin sun tashi tsaye domin kawo sauyi a siyasar kasashen nasu. Sai dai duk da wannan ikirari na matasan da ke nuni da cewa suna zargin shugabanninsu ko kuma tsofaffin da hanasu rawar gaban hantsi, a ganin  Mr. Anthony Sani da ya kasance tsohon dan siyasa da yaga jiya ya ga yau a Tarayyar Najeriyar, matasan na wannan lokaci ne suka kasance har kawo yanzu basu farka daga bacci ba. Bincike ya nunar da cewa ba wai matasan ne kawai aka bari a baya ba a harkokin siyasar Najeriyar, har ma da mata da nakasassu.