1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattauna rikicin Madagaskar na neman cijewa

April 29, 2010

Taron sasanta rikicin siyasar Madagaska na fiskantar tseko.

https://p.dw.com/p/N9Ae
Masu shiga tsakanin rikicin MadagaskarHoto: picture-alliance/ landov

Ɓangarorin da ke gaba da juna a rikicin siyasar tsibirin Madagaskar na ci gaba da kawo tseko a taron samar da maslaha da ke gudana a birnin Pretoriya na Afirka ta kudu. Hamɓaren shugaba wato Marc Ravalomanana na ci gaba da gindaya sharaɗin komawa kan karaga kafin ya zauna akan teburin tattaunawa. Yayin da Shugaba Andry Rajoelina da ke riƙe da madafun iko ke ci gaba da jajircewa kan kafa gwamantin haɗin kan ƙasa.

Shugabannin ƙasashen Afirka ciki har da Joaquim Chissano mai shiga tsakanin za su ci gaba da ganawa da sauran masu faɗa a ji na tsibirin na Madagascar a yau ɗin nan da nufin laulubo hanyoyi mayar da ƙasar kan turbar demokaraɗiya. Tun ƙarshen shekara ta 2008 ne, tsibirin na Madagaskar ya faɗa cikin wani rikici na siyasa da ya kai ga kifar da gwamantin Marc Ravalomanana.

Mawallafi: Mouhamadou Awal 

Edita: Yahouza Sadissou