1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

200708 Madrid Konferenz

Philipp, Peter (DW)July 24, 2008

Babban taron Madrid kan addinai ya samu halarcin wakilai kimanin 200 daga sassa daban daban na duniya.

https://p.dw.com/p/EivJ
Sarki Abdullah da ministocinsaHoto: AP

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka, barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na Taɓa Ka Lashe, shirin da ke duba batutuwan da suka shafi addinai, al´adu da zamantakewa tsakanin al´ummomi daban daban a wannan duniya ta mu.

A ƙarshen mako ne a birnin Madrid na ƙasar Spain aka kammala taron ƙasashen duniya dangane da samun fahimtar juna da kyautata tuntuɓar juna tsakanin addinai da ala´adu daban daban a duniya. A ƙarshen taron na yini uku wanda Sarki Abdullah na Saudiya danƙawa ƙungiyar ƙasashen musulmin duniya nauyin shiryawa, an yi kira da a ɗauki matakan daƙile ayyukan tarzoma da tashe tashen hankula. A cikin shrin na yau za mu duba yadda taron ya kaya ne.

Sama da mutane 200 daga ko-ina ciki duniya suka halarci taron na birnin Madrid. Daga ciki kuwa har da wakilai na Musulmi da Kiristoci da Yahudawa da Bhudda da kuma sauran wakilan ƙungiyoyin addini waɗanda a ƙarshe suka yi kira ga ƙasashen duniya da su haɗa ƙarfi wajen yaƙi da ´yan tarzoma. Sun yi watsi da batun nan da ake yi dangane da wata gwagwarmaya tsakanin al´adu ko addinai. Maimakon haka sun nuna aniyarsu ta ƙarfafa girmama al´adun juna da samar da kyakkyawan yanayin fahimtar juna tsakanin al´umomi daban daban.

Mahalarta taron sun amince da su ci-gaba da gudanar da irin wannan tattaunawa a kan wani ginshiƙin nuna juriya da fahimtar juna a ƙarƙashin hulɗar dangantaku tsakanin ƙasa da ƙasa. A dangane da haka an shirya gudanar da jerin tarurruka shigen wannan don ƙarawa juna sani musamman a fannonin al´adu, ilimi, zamantakewa da kuma na aikin jarida.

Ganin cewa shawarar gudanar da irin wannan babban taro ta fito ne daga ƙasar Saudiyya mai ra´ayin mazan jiya ya sa wasu suna saka ayar tambaya bisa manufar wannan taro. To sai dai Saleh Al-Namah muƙaddashin ministan al´adu da yaɗa labaru na Saudiyya ya ce bai ga wani dalilin nuna shakku ba.

“Bai kamata mu sakarwa masu matsanancin ra´ayi mara ba ko na misƙala zarratin ba. Manufarmu ita ce a yi watsi da su. Addini da ilimin falsafa sun tanadi girmama al´adu da mutunta bil Adama gaba ki ɗaya. Sun tanadi kare kadarorinsa da kare mutuncin mata da maza da na iyali gaba ki ɗaya. Muna buƙatar haka. Muna ganin idan ana son a samu wanzuwar zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin addinai to ya zama wajibi a fara gudanar da irin wannan tattaunawa don samar da zaman lafiya tsakani.”

Al Namah ya goyi da bayan shawarar yin amfani da addini a matsayin hanyar maganin matsaloli irin na matsanancin ra´ayi, bayan da a aka daɗe ana ɗaukar addini a matsayin tushen tsauraran ra´ayoyi.

“Ko shakka babu wannan shawarar ce mai kyau kuma mai ƙarfafa guiwa. Sarki Abdullah dattijo ne na ƙwarai. Ba ya da wata manufa ta daban game da kiran wannan taro. Mutum kirki ne wanda a kullum ya ke son daɗaɗawa sauran ´yan´uwansa ´yan Adam.”

Waɗannan kalaman daga bakin wannan minista dake zama tamkar wata farfaganda ga gidan sarautar na Saudiya, ya samu goyon baya daga wani wanda halartarsa a gun taron ya ɗauki hankalin jama´a, wato David Rosen, Bayahuden Amirka wanda kuma shi ne ɗan Isra´ila guda ɗaya tilo da ya halarcin wannan taron. David Rosen ya bayyana taron da cewa wani gagarumin al´amari ne na tarihi.

“Lalle ya kasance wani abin tarihi domin ya ƙunshi dukkan ɓangarorin da abin ya shafa. Ko shakka ba bu wannan taron yana da muhimmanci musamman ganin saboda ya samo asali ne daga ƙoƙarin Sarkin Saudiyya da kuma ƙungiyar musulmi ta duniya. To amma a ƙarshen muhimmancinsa zai dogara ne kan ko za a ci-gaba da gudanar da taron bayan na birnin Madrid.”

Shi ma David Rosen na mai ra´ayin cewa addini zai taka wata muhimmiyar rawa bisa manufar ɗinken ɓarakar da ake samu tsakanin al´ummomi daban daban, inda ya yi magana dangane da batutuwa na yau da kullum kamar sauran mutanen da ke ɗaukar kansu a matsayin waɗanda ba ruwansu da kowane addini.

“Addini ya na da ta cewa dangane da ƙalubalolin wannan zamani. Hatta wanda bai da wani addini ya kan karkata ga addini domn samun wata alƙibla. Yanzu muna fuskantar ƙalubaloli waɗanda ke barazana ga wanzuwar wannan duniya ta mu wato kamar matsalar ɗumamar doron ƙasa da kare muhalli, fasahar sauya ƙwayoyin halittu, ci-gaban kimiyya da matsalolin talauci. Dole ne dai mu yi aiki da hikima ta addini da al´adu don tinkarar waɗannan batutuwan.”

Ga Saudiyya dai taron ma matsayin wata dama ta wanke kanta daga illolin da hare haren 11 ga watan Satumban shekara ta 2001 suka janyo mata kasancewar da yawa daga cikin waɗanda suka kai harin ´yan ƙasar ta ne. To amma Sarki Abdullah ya duƙufa a ƙoƙarin samun fahimtar juna, inda tuni ya gana da Paparoma sannan a wani babban taro da ya gudana baya bayan nan a Makkah ya yi ƙoƙarin rage giɓin dake akwai tsakanin ´yan Sunna da ´yan Shi a.

Jamus ba ta samu babban wakilci a taron ba domin Bishop Huber da Hans Küng ba sun ƙauracewa taron, amma wakilan majalisar tsakiya ta musulmin Jamus sun halarta. Shugabanta Ayyub Axel Köhler ya yi gargaɗi game da sanya dogon buri ga taron. Ya ce muhimmin abu shi ne haɗuwar da aka yi tsakanin wakilan addinai daban daban waɗanda ma ba su san juna ba. Duk da cewa an fi shirya tarukan tuntuɓar juna tsakani a nan Turai inda ma ake magana game da wani tsarin addinin musulunci da ya dace da al´adun Turawa amma hakan bai gamsar da Köhler ba. Ya ce duk da cewa shawarwarin sun wuce batun addinin musulunci amma burin da aka sa gaba ya bambamta.

“Abin da aka sa gaba shi ne kandagarkin rigingimu. Amma ba a koyar da wani ko a canza shi ba. A nan ana batu ne dangane da fahimtar juna. Kuma muhimmin abu shi ne samun zaman lafiya. A nan kuwa addinai ka iya ba da gagarumar gudunmawa. Ina karyata masu cewa addini ne musabbabin yaƙe yaƙe.”