1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawar sulhu-Amurka da Iran

May 28, 2007
https://p.dw.com/p/BuKc

Jakadun Amurka da Iran a Iraqi sun gudanar da wata tattaunawa ta keke da keke, kann al´amurran dake faruwa a Iraqi.

Wannan dai shine karo na farko, a tsawon shekaru 27 da suka gabata, da jami´an kasashen biyu, suka gudanar da wata ganawar diplomasiyya.

Dangantaka dai a tsakanin kasashen biyu tayi tsamari ne, a lokacin da wasu yan Iran sukayi garkuwa da wasu Amurka 50 na tsawon wani lokaci, kafin sako su ,a shekara ta 1980.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa tattaunawar a tsakanin Jakadan na Amurka Mr Ryan Crocker da takwaran sa na Iran Mr Hassan Kazemi, tattaunawa ce data bude sabon babin dawo da dangantakar diplomasiyya a tsakanin kasashen biyu.

Amurka dai a baya tasha zargin Iran da haddasa rigingimu dake faruwa a kasar ta Iraqi, to amma Iran din tasha musanta wannan zargi.