1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawar sulhu ta ci tira a Kwango

Yusuf Bala Nayaya
December 24, 2016

Fata dai na kawo karshen fadawa rikicin siyasa mai muni a Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango gabanin Kirsimeti ya gushe abin da ke zuwa bayan wani zama da aka kwashe baki dayan daren Juma'a ya gaza cimma komai.

https://p.dw.com/p/2Uq10
Kongo Präsident Joseph Kabila
Hoto: imago/Xinhua

A ranar 20 ga watan nan na Disamba ne dai Shugaba Kabila ya cika wa'adinsa na biyu da ke zama na karashe ya mika mulki kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada, amma yinsa kememe ya bar mulkin ya jawo zanga-zanga da ta yi sanadi na rayukan mutane 40 kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta nunar.

Shugabannin Cocin Katolika masu fada a ji a kasar ta Kwango sun jagoranci zaman sulhu a tsakanin 'yan siyasar kasar da gabatar da wani daftari da zai sanya Shugaba Kabila ya sauka daga mulki a shekara mai zuwa, a yi sabon zabe. Sai dai fitar mahalarta tattaunawar tun da misalin karfe 05:30 na safiya agogon kasar ba tare da sake komawa ba da misalin sha daya da aka tsara, ya sanya an sake komawa ruwa, fargabar fadawa rikici da kasar ta sha gani a baya ta dawo sabuwa.

Abin da ake gani dai kawo yanzu manyan 'yan siyasar kasar ke zagon kasa ga kokarin da cocin ke yi a fadar wani fada da bai so a bayyana sunansa ba.