1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawar sulhun warware rikicin nukiliyar kasar Iran

January 26, 2006
https://p.dw.com/p/BvAj

Kasashen Sin da Iran sun nuna amannar su da kokarin da kasar Russia keyi na warware rikicin nukiliyar kasar Iran.

Wannan kalami dai yazo ne bayan da wakilan kasashen biyu suka gana a can birnin Beijing na kasar ta sin.

Kamfanin yada labaru na Reuters ya rawaito, wakilin kasar ta Iran a kokarin wannan sasantawa, wato Ali Larijani na fadin cewa, akwai sauran tsalle game da batun da kasar ta Russia ta gabatar musu, na sarrafa sanadarin Uranium din kasar ta Iran a Russia.

Shi kuwa kakakin ma´aikatar harkokin wajen kasar ta Sin wato Kong Quan cewa yayi, wannan mataki da kasar ta Russia ta dauka abu ne da zai kawo karshen takaddamar da kasashen yamma keyi akan nukiliyar kasar ta Iran.

Ya zuwa yanzu dai dukkannin kasashen biyu, wato Russia da kasar Sin sun yi watsi da kiraye kirayen da wasu kasashen keyi na kakabawa kasar ta Iran takunkumi.