1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

160910 Nahost Frieden

September 16, 2010

Ƙoƙarin Amurka na ɗorewar tattaunawa tsakanin Abbas da Netanyahu

https://p.dw.com/p/PDXH
Hoto: picture-alliance/dpa

Amurka ta hakikance cewar bayan tattaunwar kwanaki biyu tsakanin shugaban yankin Palastinawa Mahmoud Abbas da Priministan Izraela Benjamin Netan yahu, akwai alamun cimma yarjejeniya dangane da tsayar da gine-ginen yankunan Yahudawa 'yan kama wuri zauna dake gabar yamma da kogin Jordan, wanda wa'adin ke cika a ranar 26 ga watan Satunbar da muke ciki.

Mai shiga tsakani wajen warware rikicin yankin gabas ta tsakiya watau Amurka, ta bayyana tattaunawar kwanaki biyu a jere tsakanin shugaban Palastinawa Mahmoud Abbas da Priminista Benjamin Netanyahu na Izraelan a matsayin nasara. Kamar yadda sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinto ta ayyana..

" Na zauna da waɗannan Mutane guda biyu. Yanzu haka sun fara gudanar da aiki, kuma sun fara tin karar ainihin inda matsalar take, wanda za a iya cimmawa ne kaɗai ta hannayr tattaunawar kai tsaye tsakaninsu"

Symbolbild Clinton Abbas und Netanjahu
Hoto: DW-Montage/AP/picture-alliance/dpa

Ana muradin ganin cewar wannan tattaunawa za ta cigaba da gudana tsakaninsu a 'yan makonni masu gabatowa. Inda tawagar wakilan ɓangarorin biyu za su sake gudanar da Taro.  Shi ma jakadan Amurka na musamman a yankin gabas ta tsakiya George Mitchel, cewa yayi tun da aka kaddamar da wannan tattaunawar kai tsaye, ya san cewar Abbas da Netanyahu suna muradin ganin cewar an warware wannan rikici tare da cimma madafar zaman lafiya a yankin  nasu.

Ya ce akwai cigaba da aka samu kawo yanzu, harda batun tsayar da ginin matsugunnen Yahudawa 'yan kama wuri zauna da Izraela take yi a gaɓar yamma da kogin Jordan.

A ranar 26 ga watan Satumban da muke ciki nedai wa'adin dakatar da gine-ginen zai cika, kuma tuni shugaban Palastinawa Mahmoud Abbas da tawagarsa suka yi barazanar janyewa daga tattaunwar sulhun, idan har Izraela bata tsayar da ginin matsunnen yahudawan ba. Batu da Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta ce da sauran rina a kaba.

George Mitchell / Nahost / Jerusalem / USA
Hoto: AP

A karshen ganawar tasu dai Abbas da Netanyahu sun yi fatan za' a cimma zaman lafiya tsakanin al'ummomin Izraela da na Palastinu da ke wannan yanki.

To sai dai wa mazauna yankin kudancin Izraela wannan ba rana ce ta zaman lafiya ba, domin a daidai lokacin da wannan tattaunawa ke gudana a birnin kudus, 'yan Hamas sun harba musu makaman Rokoki guda biyu da Gurneti tara. Harin dai na mai zama martani ga sojojin Izraela dangane da boma-bomai da suka jefa zuwa bututun da 'yan Hamas ke yin fasa kwaurin makamai zuwa yankin, harin da ya kashe Bapalastine guda.

A yau ne aken saran jakadan Amurka George Mitchell zai je Damaskus, kafin gobe Juma'a ya shige zuwa birnin Beirut, domin tattaunawa da magabatan Syria da Lebanon dangane da cigaban da aka samu kan tattaunawar rikicin yankin na gabas ta tsakiya.

A yau ɗin ne kuma Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton za ta gana da shugaban yankin Palastinawa Mahmoud Abbas a birnin Ramallah.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita           : Umaru Aliyu