1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tauraron dan Adam yana da muhimmanci a kan harkokin sadarwa

Suleiman BabayoAugust 12, 2015

Tauraron dam Adam yana tafiya tare da yadda duniya take juyawa inda yake taimakawa kan harkokin sadarwa da na kafofin yada labarai

https://p.dw.com/p/1GERh
Galileo Satellitenprogramm
Hoto: AP/ESA

Tauraron dan Adam wata na'ura ce da aka kirkira wadda ake harbawa sararin samaniya, domin karban sako daga wani bangare na duniya zuwa wani bangare na duniyar. Masana sun fahimmci yadda shimfidar duniya take kuma suna amfani da wannan fasaha wajen inganta harkokin sadarwa.

Tauraron dan Adam yana tafiya tare da juyawar duniya ana harba shi ya zauna a wajen duniya, kuma da shi ke amfani kan sadarwa da sakonnin kafofin yada labarai. Galibi yazu tauraron dan Adam yana amfani da hasken rana. Tauraron dan Adam yana zama a wajen da ya kai nisan kilo-mita 30,000 zuwa 60,000 tsakanin sa da duniya.