1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tawagar Au ta isa kasar Mauritaniya don samo bakin zaren

Ibrahim SaniAugust 9, 2005

Juyin juya hali na gwamnati a Mauritaniya ya haifar da kace nace a tsakanin sojin kasar da suka yi juyin mulkin da kuma kungiyyar tarayyar Africa

https://p.dw.com/p/Bvaa
Shugaba Obasanjo na Nigeria
Shugaba Obasanjo na NigeriaHoto: dpa

Ya zuwa yanzu dai wannan tawaga dake karkashin jagorancin ministan harkokin wajen Nigeria wato Ambassada Olu Adeneji na kasar ta Mauritaniya.

A lokacin wannan ziyara ta tawagar ta Au a kasar ta Mauritaniya, za a gudanar da tattaunawa ne a tsakanin ta da kuma sojin da suka hambare gwamnatin shugaba Taya, bisa kokarin ganin an mutunta dokar dake kunshe a cikin kundin tsarin mulkin kasar, ta hanyar dawo da tsohon shugaba , wato Maawuya Ould taya akan mukamin sa.

Kafin dai isar wannan tawaga ta Au a kasar ta Mauritaniya, gidan talabijin na Al Arabiyya ya rawaito shugaba Ould Taya na umartar jamian tsaro na kasar dasu dauki matakin gaggawa na kakkabe tsagerun da suka aikata wannan aiki na haramun don komowa izuwa gida da kuma ci gaba da gudanar da mulkin sa.

Ould taya wanda ya fadi hakan a can Janhuriyar Niger inda yake gudun hijira bayan kifar da gwamnatin nasa, lokacin yana Saudi Arabia, yaci gaba da cewa yayi matukar mamakin yadda akayi wadanda aka dora musu alhakin kare dokokin kasa da kuma lafiyar alumma sune suka aikata wannan danyan aiki.

Rahotanni dai daga kasar na nuni da cewa kwanaki kadan bayan gudanar da wannan juyin mulkin, hukumar sojin koli ta kasar ta umarci tsohon faraminista a lokacin mulkin shugaba Taya daya kafa gwamnatin wucin gadi, wacce zata shafe shekaru biyu a gadon mulkin, wanda a lokacin suka yi alkawarin gudanar da zabe na gama gari don mika mulki ga zababbiyar gwamnati.

Bugu da kari rahotannin sun kuma tabbatar da cewa da yawa daga cikin yan kasar ta Mauritaniya sun yi lale marhabin da wannan juyin mulki, bisa irin mulkin kama karya da tsohon shugaba Taya ya gudanar na tsawon kusan shekaru ashirin da suka gabata.

Idan dai za a iya tunawa awowi kadan da gudanar da wannan juyin mulkin kasashe irin su Amurka da kungiyyar tarayyar Turai da kuma ta Africa suka yi Allak wadai da wannan al,amari da cewa ya take dokar kundin tsarin mulkin kasar.

Da alama kuma wannan batun ne ya haifar da tura wannan tawaga ta Au izuwa kasar don duba yiwuwar samo bakin zaren.

Wannan tawaga dai ta Au an shirya cewa a lokacin wannan ziyara zata sadu da Kanal Ely Ould Mohd Vall, daya daga cikin shugabannin sojin kasar dake fafutikar kare mulkin dimokradiya.

Bisa kuwa dokar dake kunshe cikin wannan kungiyya ta Au na kin yarda da gwamnatin da aka kwata da karfin tuwo, tuni ta dakatar da kasar ta Mauritaniya daga cikin yayan ta halak, har zuwa lokacin da aka mutunta wannan doka.

Tuni dai shugaban kungiyyar ta Au,wato Shugaba Obasanjo na Nigeria ya fara tuntubar wasu shugabannin na Africa game da wannan batu don ganin yadda za a warware shi cikin ruwan sanyi ba tare daci gaba da shahara ba.