1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tawagar farko da sojojin kiyaye zaman lafiya na Afrika ta isa Somalia.

March 6, 2007
https://p.dw.com/p/BuQY

A ranar Talatan nan tawagar farko ta sojin kiyaye zaman lafiya na ƙungiyar gamaiyar Afrika daga ƙasar Uganda suka sauka a birnin Mogadishu. Cike da murna da annashuwa aka tarbi jirage biyu na sojin kiyaye zaman lafiyar a filin jirgin sama na Mogadishu. Babban kwamnadan Hafsan sojin Somalia Abdullahi Omar Ali da Ministan alámuran cikin gida na ƙasar tare da kwamandojin sojin Habasha suka tarbi tawagar sojojin. Wannan dai ita ce tawagar farko ta sojin kiyaye zaman lafiyar na ƙungiyar Afrika da suka isa birnin na Mogadishu domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a ƙasar.