1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tawagar haɗin gwiwa tsakanin UN da Au ta isa yankin Darfur

June 13, 2006
https://p.dw.com/p/BuuB

Tawagar haɗin gwiwa tsakanin Majalisar Ɗinkin Dunia, da Ƙungiyar gamayya Afrika ta isa yankin Darfur, na ƙasar Sudan, da burin tantana yiwuwar aika dakarun shiga tsakanin na Majalisar Ɗinkin Dunia.

Mataimakin sakataren Majalisar Ɗinkin Dunia, mai kula da harakokin tsaro, Jean Marie Gueheno,da kuma komishinan AU, mai kulla da wannan fanni, Said Jinnit,za su tantana da tawagogin yan tawaye, da zumar cimma daidaito a kan batun.

To saidai ya zuwa yanzu, hukumomin Khartum, na ci gaba da bayyana adawa da matakin.

Majalisar Ɗinkin Dunia, ta ambata aika tawagar sojoji ta mussamman, a farkon shekara ta 2007, wada zata cenji rundunar AU, da ya zuwa yanzu, ta kasa shawo kan matsalolin yankin.

A ɗaya wajen kuma, yau ne, a ke sa ran hawa tebrin shawara tsakanin gwanatin Sudan, da yan tawayen gabacin ƙasar, a birnin Asmara na ƙasar Erythrea.

Saidai ƙungiyar tawayen JEM, ta yi ƙorafin cewar an mayar da ita saniyar ware, a cikin tantanawar.