1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tawagar kasar Sin ta kai ziyara Darfur

April 8, 2007
https://p.dw.com/p/BuO6

Wata tawagar jamian gwamnatin kasar China ta kai ziyara sansanonin yan gudun hijira na darfur a kasar Sudan domin duba halinda ake ciki a yankunan.

Kasar ta China wadda ke kann gaba wajen cinikin man fetur na Sudan wadda kuma take da ikon darewa kujerar naki a komitin sukhu na MDD,tana fuskantar suka daga kasashen yamma da suke zarginta da yin watsi da batun aikewa da sojojin MDD zuwa Darfur ba tare da amincewar gwamnatin Khartoum ba.

Tawagar ta ziyarci sansanonin Abu Shouk da Nyala.

A makon daya gabata ministan tsaro na China Cao Gangchuan ya mikawa Sudan tayin karfafa hadin kai a fannin aiyukan soji yana mai kira ga Sudan sdata amince da shawarar da tsohon sakataren MDD Kofi Annan ya bayar game da sasanta rikicin yankin Darfur.