1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

TawagarMajalisar dinkin duniya ta isa Sudan

June 6, 2006
https://p.dw.com/p/BuvG

Wata tawagar majalisar dinkin duniya ta isa kasar Sudan inda zata tattaunawa da jamian gwamnatin Sudan dangane da batun halin da jamaar yankin Darfur suke ciki da kuma bukatar aikewa da dakarun majalisar domin taimaka shirin zaman lafiya.

A watan mayu ne dai,Sudan dai ta sanya hannu akan yarjejeniyar zaman lafiya da babbar kungiyar yan tawaye ta Darfur ,kuma tun daga wancan lokaci,kasashen duniya suna ci gaba da kokarin janyo hakalin kasar ta Sudan da ta amincewa majalisar dinkin duniya ta karbi ragamar samarda zaman lafiya a a yankin daga hannub dakarun kungiyar taraiyar Afrika su 7,000.

Gwanmatin Sudan dai ta amince da ziyarar,wata tawagar jamian sojin majalisar dinkin duniya zuwa Darfur,domin su tsara aiyukan zaman lafiya na sojin majalisar.

Wannan shine karo na farko da akayi maraba da wata tawagar majalisar a Sudan.