1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

TB Joshua yaki zuwa kotu

Yusuf BalaNovember 30, 2015

Babbar kotu a Legas karkashin mai shari'a Coroner Oyetade Komolafe ta dora alhakin mutuwar mutane sama da 100 mafi yawa daga kasar Afirka ta Kudu kan shugaban cocin da masu aikin gini.

https://p.dw.com/p/1HEp5
Synagogue Church of All Nations in Lagos Ruine 13.09.2014
Ginin majami'ar da ya rushe da halaka mutane sama da dariHoto: picture alliance/AP Photo/Sunday Alamba

A Najeriya fitaccen malamin majami'ar nan TB Joshua, tare da masu aikin kwantiragi biyu da ke fiskantar laifin nuna rashin kulawar da ta dace a wani katafaren ginin majami'a da ya rushe a Legas, tare da halaka mutane 116 sun ki bayyana a gaban kotu, abin da ya sanya alkali mai sauraren karar ya dage shari'ar zuwa wani lokaci.

Babbar kotu a Legas karkashin mai shari'a Coroner Oyetade Komolafe ta dora alhakin rasa rayukan mutane sama da dari a ranar 12 ga watan Satimba na shekarar 2014 a majami'ar church of All Nations wato ta TB Joshua tare da wasu injiniyoyi biyu da suka jagoranci ginin dakunan karbar baki mai hawa shida wanda aka gina ba bisa kaida ba, rushewar ginin ta halaka wadannan mutane wadanda mafi yawa sun fito daga kasar Afirka ta Kudu.

Mai shari'a Lawal Akapo ya nuna rashin jin dadi na gaza bayyanar wadanda a ke zargi inda ya ce kotu na bukatar a bada adireshi na wadannan injiniyoyi cikin sa'oi 72 sannan za a sake zama sauraren shari'ar ranar 11 ga watan Disamba.