1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tchad za ta tura dakarun a Jamhuriya Afrika ta tsakiya

November 17, 2006
https://p.dw.com/p/Bubd

Ƙasar Tchad, ta bayyana aika rundunar kwantar da tarzoma, a makwabciyar ta, Jamhiurya Afrika ta tsakiya, domin taimakawa dakarun wannan ƙasa, su furgaɗi yan tawayen.

Praministsan ƙasar Tchad Pascal Yoadimnaji, ya zargi Sudan ta cinna wutar rikici a Jamhuriya Afrika ta tsakiya.

A halin da ake ciki dai, yan tawayen na ci gaba, da mamaye ƙarin yankunan ƙasar.

Bayan birnin Birao,yanzu su na darkakawa, zuwa birnin Bria, dake tazara kilomita 600, arewa maso gabancin Bangi babban ƙasar.

A wani rahoto kuma, da ta bayyana ƙungiyar bada agaji da Oxfam, ta nuna damuwa a game da ƙaruwar jama´a, a sanssanonin yan gudun hijira na Tchad,a sakamakon tashe-tashen hankulan ƙabilaci,da ke ci gaba da ɓarkewa , a wasu yankunan ƙasar.

Oxfam ta yi kira, ga ƙungiyoyin bada agaji, su dubi matsalolin wannan jama´a, da idon rahama, ta hanyar aika masu ababen more rayuwa.