1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tedros Adhanom na Habasha na neman kujerar hukumar WHO

Kamaluddeen SaniMay 24, 2016

Ministan harkokin wajen Habasha Tedros Adhanom ya kaddamar da yakin neman tsayawa takarar shugabancin hukumar lafiya ta duniya a ranar talatar nan,

https://p.dw.com/p/1Ito4
Äthiopische Rückkehrer aus Jemen Theodros Adhanom Interviewpartner
Hoto: DW/T. Getachew

Tedros Adhanom wanda ya jaddada cewar lokaci ya yi da dan Afirka ya dace ya jagoranci hukumar.

Tedros ya fadawa manema labarai a Geneva cewar nahiyar zata bayar da tata baiwar domin kara inganta harkokin lafiya a Duniya a yayin da yake nuna muradinsa na maye gurbin Margaret Chan ta Hong Kong da ke shirin barin mukamin a shekarar mai zuwa.

Kazalika Tedros mai shekaru 51 da ke zama kwararran likita ya kuma ce baya ga rike manyan mukaman kasa da kasa kan harkokin lafiya zai kuma taimaka wajen yaki da cutar Aids da cutar tarin fuka da maleriya a sauye-sauyen da zai kawo.

A baya ga Tedros Adhanom akwai karin 'yan takara irin su Philippe Douste Blazy dan Faransa gami da dan kasar Pakistan Sania Nistar.