1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Teku mafi Girma

Abba BashirMay 29, 2006

Tekun da ta fi Girma a Duniya

https://p.dw.com/p/BvVQ
Tekun Pacific
Tekun PacificHoto: dpa

Jama’a masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na amsoshin takardunku,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya:Fatawarmu ta wannan makon ta fito daga hannun Malama A’ishatu Bature,daga Jihar Kadunan Tarayyar Najeriya. Malamar cewa ta yi, bayan gaisuwa mai yawa a gare ku,don Allah ina so ku amsa min wannan tambaya tawa, tambayar kuwa ita ce ; Shin, wace Teku ce mafi girma a wannan Duniya tamu?

Amsa : To Malama A’isha , Tekun Pacific ita ce Teku ma fi girma a wannan Duniya ta mu , domin kuwa Tekun ta pacific ta kwashe fiye da kashi 45 bisa dari na yawan tekun da ke fadin wannan Duniya.Tekun dai tana da tsawo na murabba’in kilomita 166,241,700 fadinta kuwa da aka auna daga inda ya fi girma , sai da aka samu cewa tana da fadin kilomita 17,700. Ta bangaren zurfi kuwa tana da zurfin kafa 12,925.

Wannan Duniya dai ta hada doron-kasa kasa ne da kuma Ruwa, wanda ya hada da ruwan Tekuna, Tafkuna da kuma Koguna, to amma masana ilimin Taswirar Duniya sun tabbatar da cewa yankin da ruwa ya mamaye a doron Duniya yafi yankin da Kasa ta mamaye yawa.Masanan sun tabbatar da cewa, idan aka kasa wannan Duniya zuwa kashi goma (10), to kaso bakwai (7) gabadaya Ruwa ne, sauran kaso uku (3) kuma Kasa ce da Rairayi da kuma Duwatsu, kuma daga cikin wannan kashi bakwai (7) da Ruwa ya mamaye,kaso shida na Ruwan,Ruwan zartsi ne,kaso daya(1) kuma Ruwan dadi, wato ruwan da ake amfani da shi wajen sha da abinci da kuma ibada. Har ila yau dai idan aka dauki wannan kaso da Ruwa ya mamaye da ga fadin wannan Duniya tamu, ka sake kasa shi gida uku(3) to kaso daya bisa ukunnan (1/3) Tekun Pacific ce ta mamaye shi,sauran kashi (2/3) kuma shine ta barwa su Bahar maliya,su Tekun Atlantic,su Tekun fasha,su Tekun Niluna kasar Masar da kuma Tafkuna irin su Tafkin Chadi,su Tafkin Baikal na Kasar Rasha da dai sauran Tafkuna da Tekuna da kuma Koguna da ke fadin wannan Duniya.

Masana ilimin Kimiyya da kuma na sha’anin Ruwan Teku sun tabbabtar da cewa “A cikin kogi dai akwai Ruwa iri biyu,ruwan dadi da na zartsi, gasu dai a cikin kogi guda daya to amma akwai maraba a tsakaninsu, ba su cakuda sun hade da juna ba saboda wannan kariya da Allah ya yi a tsakaninsu. In da ruwan dadi ya ke idan aka debi wajen aka dandana za a ji dadi sak ba wani gauraye, inda kuma na zartsi ya ke namma idan aka debeshi aka dandana za a ji zartsi sak ba wani gauraye.