1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tilastawa yara aikin soji a Sudan ta Kudu

October 27, 2016

Kungiyar SPLA ta sako yara kanana dake aikin soji kimanin 145 bayan shigar tsakani da MDD ta yi, inda aka sako yaran a jihar Jonglei

https://p.dw.com/p/2Rl9S
Kindersoldat Südsudan
Hoto: picture-alliance/dpa/S.Bor

A cewar asusun kula da yara na MDD wato UNICEF lamarin sako wadannan da aka tilastawa shiga yaki, sakin nasu ya faru ne a shekaran jiya Talata. Asusun ya kuma yi kira ga dukkan bangarorin da ke gaba da juna, da su daina daukan yara kanana ana tilastasu shiga aikin soji. Yaran dai an sako ne daga bangaren mayakan 'yan tawayen SPLA wadanda ke biyayya ga Riek Machar, da kuma wani bangaren mayaka da ake kira Copra, wadanda suka sa hannun zaman lafiya da gwamnati a bariya. An sako yaran ne a jihar Jonglei da ke arewa maso gabashin Juba babban birnin kasar.