1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Togo: Taron nuna goyon bayan gwamnati

Salissou Boukari
August 28, 2017

Kawancen jam'iyyun da ke mulki a kasar Togo sun nemi kira wata zanga-zangar ta tsawon kwanaki uku daga ranar Talata don nuna goyon bayansu ga Shugaban kasar ta Togo Faure Gnassingbé.

https://p.dw.com/p/2iyO5
Faure Gnassingbe
Hoto: AP

Shugabannin jam'iyyun da ke mulki a Togo din dai sun ce kiran wannan zanga-zanag na da nasaba da yunkurin da su ke yi na nuna goyon bayansu ga shugaban kasar mai ci Faure Gnassingbé. Gilbert Bawara da ke cikin wadanda suka kira wannan zanga-zanga ta kwanaki uku ya ce ''mu burinmu shi ne na ganin kasarmu ta samu aiwatar da sauye-sauye na siyasa na gaba daya bayan dogon nazari wanda kuma kowa zai aminta da shi."

Proteste in Togo gegen Gnassingbe ARCHIV
'Yan adawa a Togo na sun hukumomi su gudanar da wasu sauye-sauye na siyasaHoto: picture alliance/AA/ Alphonse Ken Logo

Wannan jerin gwanon da jam'iyya mai mulki ta kira dai wani martani ne ga tsarin da 'yan adawan kasar suka yi na gudanar da jerin gwano na kwanaki biyu a kasar domin tilastawa shugaban kasar aiwatar da sauye-sauye na siyasa a kasar da ma batun zaben 'yan kasar ta Togo da ke kasashen waje. Jean Pierre Fabre shi ne madugun 'yan adawan kasar ta Togo ya kuma shaidawa DW cewar su ma yanzu sun shirya na su jerin gwanon inda ya kiara da cewa ''ina fatan dai ba za mu arangama a bisa tituna ba.''

Wannan hali dai da aka shiga na tada jijiyoyin wuya a tsakanin 'yan siyasar kasar ta Togo na tayar da hankalin kungiyoyin fararen hular kasar. Nora Dado Amedjenou-Noviekou da ke shugabantar hadin gwiwar kungiyoyin yammacin Afirka masu fafutikar samun zaman lafiya ta ce ''ni ina ganin wata kila lokaci ya yi da bangarorin biyu za su zauna a kan teburi guda domin tattauna wannan matsala don makomar kasar ta Togo. Togo dai kasarmu ce, ya kamata ayi nazarin hanyoyin bunkasa wannan kasa ba tashin hankali ba. Idan babu zaman lafiya to komai wani batun ci gaba."