1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tony Blair ya ambata janye sojojin Britania daga Irak

February 21, 2007
https://p.dw.com/p/BuRN

Nan gaba a yau ne, a ke sa ran Praministan Britania Tony Blair, zai bayyana shirin fara janye dakarun Britania daga kasar Irak.

Kakakin fadar gwamnatin Amurika da ya tabatar da labarin ya ce Blair ya kiri shugaba Georges Bush domin bayyana masa, wannan mummunar sanarwa.

Rahotanin da jaridun Britania su ka buda a sahiyar yau sunnunar da cewa baki daya Britania zata janye sojojin ta daga Iraki kamin ƙarsehn shekara ta 2008.

Jaridun su ka ce,“ cemma ko wa ƙi jin bari, zai ji woho“.

Gwamnatin Britania ta yanke shawara janye sojojin ta, ta la´akari da matsanancin halin da ke ci gaba da wakana, a ƙasar ta Irak, sannan da matsin lambar da ta ke sha,a cikin gida.

Wannan batu na daga sahun matsalolin da, su ka zubda mutunci, da ƙimar Praminista Tony Blair, wanda a ke sa ran ma zai murabus, a yan watani masu zuwa.