1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya bada umarnin fidda rahoton FBI

Abdullahi Tanko Bala
February 2, 2018

Shugaba Trump ya bada umarnin fitar da bayanan dake ikrarin adawa da shi a hukumar binciken laifuka ta FBI.

https://p.dw.com/p/2s3Bb
USA Donald Trump erneuert Einreiseverbot
Hoto: picture-alliance/dpa/NOTIMEX/Casa Blanca

Shugaban Amirka Donald Trump ya bada umarnin fidda bayanan binciken da aka yi ta cece kuce akan su wadanda dan majalisar dokoki na jam'iyyar Republican ya rubuta da ya nuna hukumar binciken laifuka ta Amirka FBI ta saba ikonta na bincike inda ta sa ido kan daya daga cikin hadiman Trump a dangane da binciken zargin katsalandan da Rasha ta yi a zaben Amirka.

Da yake jawabi a fadar White House Trump ya tabbatar da bada umarnin wallafa bayanan, yana mai cewa mutane da dama za su ji kunya ko kuma ma sai sun raina kansu.

Trump wanda tun da farko fusata da binciken ya zargi manyan jami'an ma'aikatar shari'a wadanda wasu daga cikin su shine ya nada su da kuma hukumar FBI da maida al'amuran siyasa da ya farantawa 'yan demokrats da kuma wadanda yace basa kaunarsa a cikin Republican