1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya bukaci tattaunawa da Kim Jong Ung

Abdul-raheem Hassan
January 10, 2018

Shugaban kasar Amirka Donald Trump ya ce kofa a bude take domin shiga tattaunawa da shugaban kasar Koriya ta Arewa Kim jong Un a lokacin da ya dace a kan muhimman batutuwa da suka fi cancanta.

https://p.dw.com/p/2qeOS
Kombi-Bild  Trump und Kim Jong Un
Hoto: Reuters/K. Lamarque/KCNA

Fadar shugaban kasar Amirka ta White House ta ce Shugaba Trump ya bayyana matakin bude kofar shiga tattaunawa da shugaban kasar koriya ta Arewa a yayin zantawa da shugaban Koriya ta Kudu Moon Jae-In ta wayar tarho.

Sabon babin neman dinke barakra da ke tsakanin Amirka da Koriya ta Arewar ta biyo bayan tasirin sabunta dangantaka tsakanin shugaba Kim Jong Ung na Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu da suka shafe shekaru biyu suna wa juna kallon hadirin kaji.

Shugaban kasar koriya ta Kudu Moon Jae-In ya ce yana cike da fatan tattaunawarsu da Kim Jong Un zai bada damar tattaunawa a kan kera makaman kare dangi da Koriya ta Arewa ke sa-in-sa da sauran kasashen duniya.