1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya tabbatar zai kori baki milyan uku

November 13, 2016

Kamar yadda ya yi alkawari lokacin yakin neman zabe zababben shugaban kasar Amirka ya nanata cewa zai fidda miliyoyin bakin haure da ke zama ba izini a cikin kasar

https://p.dw.com/p/2Sdpo
USA Donald Trump designierter Präsident
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Reynolds

A hirarsa ta farko da kafafen yada labarai tun bayan nasarar da ya samu zaben shugabancin kasar, Shugaban kasar Amirka mai jiran gadon Donald Trump, ya jaddada cika alkawarin da ya yi lokacin yakin neman zabe kan korar bakin da basdu da izinin zama a kasar. Trump a wata hira da ya yi  da tasharar CBS a yau Lahdi, ya bayyana cewa da zaran ya kama mulki zai kori bakin haure miliyan uku nan take. Zabbaben shugaban kasar ta Amirka ya ce, abinda zai yi bayan kama iko shi ne, bakin da ake da shaidar suna aikata laifi da wadanda aka sansu a matsayin manyan dilolin sayar da muggan kwayoyi,  wanda ta yi wu jimillarsu ya kai miliyan biyu izuwa uku, duk za a fitar da su daga kasar ta Amirka, ko kuma a dauresu a gidajen yari. Dama dai Donald Trump ya sa batun tsaron kan iyakar kasar da Mexiko a matsayin na gaba cikin yakin neman zabensa.