1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya yi tir da yada labaran karya a kansa

January 11, 2017

Donald Trump ya yi kakkausar suka kan yada bayanan sirri da ba a tantance su a kan sa wanda ya baiyana a matsayin makirci domin bata masa suna.

https://p.dw.com/p/2VeLY
USA Donald Trump Pressekonferenz in New York City
Hoto: Getty Images/S. Platt

Shugaban Amirka mai jiran gado Donald Trump ya gabatar da taron manema labarai na farko a hukumance bayan zaben shugaban kasar da aka gudanar a watan Nuwamba. Tun da farko Trump ya rubuta a shafinsa na Twitter ya na zargin hukumomin leken asirin Amirka da kwarmata labaran karya kan dangantakarsa da Rasha, ya na mai kakkausar suka ga wasu kafofin yada labarai biyu wadanda yace sun yada labaran kanzon kurege.

Shugaban mai jiran gado ya ce ''labari irin wannan abu ne ma sam da bai kamata a rubuta shi ba, bai kamata ma a ji shi ba kuma bai kamata a wallafa shi ba.''

A waje daya kuma Trump din ya tabbatar da cewa 'ya'yansa biyu za su karbi ragamar gudanar da harkokinsa na kasuwanci bayan ya hau karagar mulki.