1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump zai sassauto da dokarsa

March 9, 2018

Gwamnatin Amirka ta ce shugaba Trump zai janye karin sunayen wasu kasashe daga harajin da ya dora kan karafan da za su rika shiga kasar da ya yi.

https://p.dw.com/p/2u4FQ
US-Präsident Trump unterschreibt Strafzölle umringt von Stahlarbeitern
Shugaba Trump yayin rattaba hannu kan dokar haraji kan karafaHoto: Reuters/Leah Millis

Gwamnatin Amirka ta ce shugaba Trump zai janye karin sunayen wasu kasashe daga harajin da ya dora kan karafan da za su rika shiga kasar da ya yi a ranar Alhamis. Sakataren Baitul Malin Amirkar Steven Mnuchin wanda ya bayyana hakan a wata hirar da ya yi da tashar CNBC, ya ce shugaba Trump zai rage wasu daga cikin kasashen ne cikin makonni biyu da ke tafe. Kashi 25 cikin dari ne dai gwamnatin Amirkar ta dora kan karafa daga ketare, yayin da kashi goma cikin dari yake a kan goran ruwa, in banda kasashen Kanada da da Mexico.

Matakin dora harajin na Mr Trump na jiya Alhamis, na ci gaba da fuskantar suka daga sassa daban-daban, musamman kasashen Turai da kuma China. Shugabar gwamnatin Jamus da ita ma ta soki matakin na Mr trump ta ce tana da kwarin gwiwar hukumar tarayyar Turai da ke shirye-shirye zama a teburi da Amirka kan batun, za ta sama wa tufkar hanci.