1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsaffi 16 sun halaka a cikin wani hari a Yemen

Gazali Abdou TasawaMarch 4, 2016

A kasar Yemen mutane akalla 16 suka rasu a wannan Jumma'a lokacin da wasu 'yan bindiga suka buda wuta a wata cibiyar ajiyar tsofaffi da ke a birnin Aden na kudancin kasar.

https://p.dw.com/p/1I7cB
16 Tote bei Angriff von Extremisten auf Seniorenheim in Jemen
Hoto: Reuters

A kasar Yemen mutane akalla 16 suka rasu a wannan Jumma'a lokacin da wasu 'yan bindiga suka buda wuta a wata cibiyar ajiyar tsofaffi da ke a birnin Aden na Kudancin kasar.

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ruwaito cewa wasu mutane ne guda hudu dauke da bindigogi suka kutsa cikin gidan ajiyar tsofaffin da ke a unguwar Cheik Othman ta birnin na Aden inda bayan sun bindige mai gadi suka yi ta yin harbin kan mai uwa da wabi a cikin cibiyar inda suka kashe tsaffin 11 da kuma wasu mata mabiya addinin Hindu da ke hidimar kula da lafiyar tsaffin a cikin cibiyar.