1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsagaita wuta tsakanin Isra´ila da Hizbollah

August 15, 2006
https://p.dw.com/p/Bumi

An shiga kwana 2 na tsagaita wuta, tsakanin dakarun Isra´ila da na Hezbollah.

Yan gudun hijira na bangarorin 2,sun yi anfani da wannan dama domin komawa matsugunan su.

In banada yan hadaruruka nan da cen a jimilce za acewa sassan 2 sun awaitar da tsagaita wutar, bayan kawanki 34 na kare jinni biri jinni.

A kasar Iran al´ummomin sunshirya shagulgullan a sakamakonabinda su ka kira nasara da Hizbolahi ta samu akan mayakan Israi´la.

Sannan shugaba Mahamud Ahmadinejdad ya ce Iran a shire ta ke ta kai farmaki ga birninTel-Aviv muddun bukatar hakanta taso.

Majalisar Dinkin Dunia ta ta samu nasara cimma wannan tsagaita wuta, ta nunar da cewa nan da yankwanaki masu zuwa, zata tura dakarunshuiga tsakani a kudancin Labanon.

GObe ne idan Allah ya kai mu za a gana tsakaninministar harakokin wajen Isra´ila Tzipi Livni da sakatare jannar na Majalisar Dinkin Dunia Koffi Annan a game da wannan batu.

A nasa gefe ministan harakokin wajen Jamus, Frank Walter Steimeir, ya kai ziyara aiki a yankin na gabas ta tsakiya inda ya ke tantanawa da hukumomin Jordan da syria a kan wannan rikici.

Shima ministan harakokin wajen wajen ƙasar France Philips Duzte-Blazy, ya koma yau a birnin Beyruth, domin tantanawa akan mattakan girke dakarun shiga tsakani na Majalisar Dinkin Dunia, a kudancin Labanon.