1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsagaita wuta tsakanin LRA da gwamnatin Uganda ta fara aiki

August 29, 2006
https://p.dw.com/p/BulH

Yau ne yarjejeniyar tsagaita wutar da a ka cimma, tsakanin yan tawayen LRA, da gwamnatin Uganda, ta fara aiki.

Shugaban kasa Yuweri Museveni, ya umurci dakarun gwamnati, su dakatar da duk wani mataki, da zai mayar da hannu agogo baya.

Wannan shine matakin farko, da zai tabbatar da wanzuwar zaman lahia a ƙasar, bayan shekaru kussan 20 na ɓarin wuta.

Yuweri Musseveni ya yi kira ga dukan rundunoni gwamnati su kuma a barikokin su.

Nan da dan lokaci ƙalilan a ke jiran jawabin shugaban yan tawayen LRA Joseph konny.

Saidai tunni, kakakin sa, Obwenyo Olweny, ya tabatar da cewa LRA a shire at ke ta mutunta wannan yarjejeniyar, kuma ba z ata aikata lefin daya ba, wanda zai sama wa matsayin da ta dauka.

Kazalika a jawabin da yayi jiya, ta kafofin sadarwa, mataimakin rundunar LRA Vincent Otti, ya bada umurni ga dakarun ƙungiyar, su shirya kwance ɗamara.

Kamar yadda yarjejeniyar ta tanada,dakarun LRA su kimanin dubu 5,za su haduwa a wasu yakuna 2 na kasar Sudan.

Saidai a jawabin da yayi Musseveni ya yi barazanar cewa muddum ba su cika alkawarin ba, gwamnati za ta ci gaba da farautar su.