1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsamin dangantaka a tsakanin Biritaniya da Russia

Ibrahim SaniDecember 13, 2007
https://p.dw.com/p/CbIX

Faraministan Biritaniya Godon Brown ya soki matakin Russia na rufe cibiyar al´adun ƙasar dake Russia Mr Brown ya ce matakin abune da ba zai taɓa saɓuwa ba, bisa irin namijin ayyukan da cibiyar take gudanarwa, a Russia da kuma ragowar ƙasashen Duniya. Daraktan cibiyar ta British Council a Russia, Mr James Kenndy, ya tabbatar da cewa matakin na Russia, abune da ka iya haifar da tsamin dangantaka, a tsakanin Biritaniya da Russia. Biritaniya dai na bukatar Russia miƙa mata tsohon Jami´in leken asiri na ƙasar wato Andrei Lugovoi, don gurfana a gaban ƙuliya. An zargi tsohon Jami´in ne da halaka ɗan majalisa Litvinenko, ta amfani da guba.To sai dai ya zuwa yanzu, mahukuntan Russia sun ƙi miƙa tsohon Jami´in na KGB ga ƙasar ta Biritaniya.