1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsananin zafi na addabar yankuna da dama a nahiyar Turai.

July 23, 2006
https://p.dw.com/p/BupR

A yankuna da dama na nahiyar Turai, ana ta fama da tsananin zafin bazara, wanda a halin yanzu ya janyo sanadiyyar mutuwar mutane 21 a Faransa, a cikinsu har da wani ɗan jariri mai watanni 15 da haihuwa. Asarar rayukan a Faransa, ta sa ana fargabar dawowar bala’in zafin nan da aka yi a cikin shekara ta 2003, wanda ya janyo mutuwar mutane dubu 15 a Faransan da kuma wasu dubu 20 a Italiya. A yau lahadi dai, an ɗan sami sassaucin lamarin a yankuna da dama na nahiyar Turan. Amma masu nazarin yanayi sun ce za a sami hauhawar ma’aunin zafi kuma daga gobe litinin har zuwa tsakiyar makon.