Tsarin Amurka a Iraki
December 13, 2006Talla
Shugaba George W Bush na Amurka ya dage sanar da sabbin manufofin kasarsa akan Iraki har zuwa shekara mai zuwa .Bayan tattaunawa da comandojin rundunar sojin kasarsa adangane da nazarin halin da Ioraki ke ciki,kakakin fadar white house John Snow,ya sanar dacewa shugaban Amurkan na neman karin bayanai ne kafin ya dauki kowane mataki.To sai dai commnda na biyu na Amurka mai barin gado a Irakin Lt Gen Peter Chiarelli ya bayyana cewa zaa iya cimma nasarn rage tashe tashen hankula a Irakin ne kadai,idan an samarwa mutane marasa aiki ayyukan yi,da inganta kayayyakin mare rayuwa,inda yayi gargadin cewa Dakarun Amurka su kadai bazasu iya cimma wannan buri su kadai ba.