1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsarin Blue Card ga baƙi masu sha´awar zuwa Turai

Mohammad Nasiru AwalOctober 31, 2007

Wannan tsari zai bawa ƙwararrun ma´aikata izinin zama da yin aiki a ƙasashen ƙungiyar EU.

https://p.dw.com/p/C167
Fratini da Barroso
Fratini da BarrosoHoto: AP

Jama´a masu sauraro barkanku da warhaka, barkanmu kuma da saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na MKT, shirin ke kawo muku batutuwan da suka shafi siyasa, tattalin arziki, al´adu, zamantakewa da kuma dangantaka tsakanin kasashen nahiyar Turai.

A halin da ake ciki a nan nahiyar Turai ana neman kwararrun ma´aikata musamman a fannonin aikin injiniya da na´ura mai kwakwalwa wato komputa da kuma masana ilimin kimmiya ruwa a jallo. A tarayyar Jamus kadai akwai guraben aiki na kwararrun ma´aikata kimanin dubu 165 da ba a cike su ba. An yi kiyasin cewa rashin cike wadannan guraben aiki na jawowa kasar ta Jamus asarar kudi wurio na gugan wuri euro miliyan dubu 20 a kowace shekara. A sauran kasashemembobin KTT ma haka abin yake. A dangane da haka hukumar kungiyar EU ta gabatar da wani tsari da ta kira Blue card don yaki da wannan matsala. Kamar tsarin Greencard a kasar Amirka, shi ma tsarin na Blue Card na da nufin janyo hankulan kwarrarun masana musamman daga Afirka da Asiya zuwa kasashen kungiyar EU. to sai dai wannan shirin ya gamu da adawa daga kasashe kamar Jamus da Austriya kamar yadda zaku ji karin bayani a cikin shirin na yau wanda ni MNA zan gabatar.

MUSIK/JINGLE

An yi kiyasin cewa kashi 5 cikin 100 ne kadai na kwararrun ma´aikata a duniya baki daya suke zuwa nahiyar Turai. Sama da kashi 50 cikin 100 sun fi sha´awar zuwa Amirka. Hukumar tarayyar Turai ta ce dalilin haka shi ne bambamce bambamce dake akwai a dokokin zaman baki a kasashen kungiyar, wanda zama wani karan tsaye ga bakin. A saboda haka yanzu ake fata tsarin na Blue card zai taimaka bisa manufa, inji shugaban hukumar EU Jose Manuel Barroso.

1. O-Ton Barroso:

“Blue card ba ya matsayin wani cek kuma ba ya nufin samun cikakken izinin zama kasa kai tsaye. Wani shirin hadin guiwa ne tsakanin kasashen Turai wanda zai yi aiki a dukkan kasashe 27 memebobi kungiyar EU.”

Tsarin ya tanadi ba wa bakin damar zama cikin wata kasar Turai tsawon shekaru 2. Baya ga hakla suna da ´yancin kawo iyalinsu sannan suna iya canza kasa a tsakanin kasashen EU. Wakiliyar gwamnatin tarayyar Jamus mai kula da zaman baki Maria Böhmer ´yar jam´iyar CDU ta yi suka da kakkausan lafazi kan shirin na hukumar mai hedkwata a birnin Brussels. Ta ce dole ne a manufofin shige da ficen bakin ya ci-gaba da zama a hannun kasashe membobin kungiyar. Ta ce shawarar hukumar ba ta dace ba, domin a nan gaba ma ko-wace kasa ce zata yanke shawara kan yawan kwararrun ma´aikata da take son ta dauka. Shi kuwa Manfred Weber wakilin Jamus na bangaren masu ra´ayin mazan jiya a majalisar Turai, saka ayar tambaya ne da cewa.

2. Weber:

“Tambaya a nan ita ce wane ne kwararren ma´aikaci? Ga tsarin mu na yanzu hakan ya dogara ne ga yawan albashin ma´aikaci. Kamata yayi a samu shaida dangane da dangantakar aikin mutu.”

Manfred Weber wanda ke goyon bayan tsarin na Blue Card to amma kamar sauran takwarorinsa shi ma yana nuna shakku.

3. O-Ton Weber.

“Idan ana maganar tsarin na Blue Card to ya zama wajibi a yi bayani a siyasance cewar duk wata wadata da za´a samu zata dogara akan wadannan mutane. A matsayin mu na masu karfin tattalin arzikin zamu samu nasara ne idan muka kasance sahun farko a gogayyar da ake yi ta mafiya ilimi.”

A saboda haka Weber na fatan cewa hukumomin birnin Brussels zasu tashi haikan wajen wayarwa da jama´a kai a game da starin na Blue Card. Ya ce bai kamata a takaita wannan batu a kan tsarin na Blue card kadai ba dole ne samo hanyoyin taimakawa wadannan kwararrun ma´aikatan don ciyar kasashen gaba musamman a aikin raya kasa bayan sun koma kasashen na asali.

A daura da shirin na EU, majalisar ministocin janhuriyar Czeck ta amince da wani kuduri da nufin dauko ma´aikata daga ketare zuwa kasar. Shirin wanda ta yiwa lakabi da Green Card ya tanadi ba da izini zama da aiki na tsawon shekaru 3 ba ma kawai ga kwararrun ma´aikata kadai ba a´a har ma da baki wadanda ba su da kwarewa kuma suke cikin kasar ba bisa ka´ida ba, inji ministan kwadago da zamantakewa na Czeck Petr Necas sannan sai ya kara da cewa.

3. O-Ton Necas:

“A daura da shirin kungiyar tarayyar Turai, daga shekara mai zuwa jamhuriyar Czeck zata fara aiwatar da shirin ba da Green Card ga baki masu sha´awar zuwa kasar.”

Shi ko yaya sauran jama´a ke daukar shirin na kungiyar EU. Ga dai ra´ayin wasu.

1. O-Ton Frau:

“A bangare daya shirin na da kyau domin zai bai da damar cike gibin da ake samu na rashin kwararrun ma´aikata, amma a daya bangaren zai haddasa rudani musamman ga tsofaffin ma´aikata wadanda ba sa samun aikin yi saboda yawan shekarunsu.”

Ita kuwa wannan matar ta na mai ra´ayin cewa ne.

3. O-Ton Frau:

“Ina ganin ba dace ba idan wata kasa ta dauko ma´aikata daga ketare, saboda rashin kwararrun ma´aikata na cikin gida. Kamata ya yi a yiwa tsarin ba da ilimi gyaran fuska.”

To ko menene ra´ayin wannan mutumin

2. O-Ton Mann:

“Ana bukatar wata manufar mai ma´ana dangane da zaman baki amma ba kayyade yawansu. Kayyade yawansu ba zai sa mun cimma burin mu ba.”

Shi ma wannan mutumin na mai ra´ayin cewa

4. O-Ton Mann:

“Wannan mummunan ra´ayi ne. Ganin yadda ake fama da matsalar yawan marasa aikin yi da kamata yayi su fara daukar Jamusawa ko kuma su ba da kudin ilimantar da Jamusawa.”