1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsarin gani na Jemage

Abba BashirNovember 27, 2006

Bayanin yadda Jemage yake iya gani

https://p.dw.com/p/BvV8
Jemage
Jemage

Jamaa masu sauraronmu assalamu alaikum, barkammu da wannan lokaci, barkammu kuma da sake saduwa da ku a cikin wani sabon shirin na wasikun ma su sauraro,shirin da yake amsa tambayoyin da ku masu sauraro kukan aikomana.

Tambaya: Fatawarmu ta wannan makon ta fitone daga hannun Malama Gambo Manu, Binji, Sokoto, Najeriya. Ta ce shin, dagaske ne Jemagu makafi ne?

Amsa : To malama Gambo, daga nan Bonn na tuntubi Dr Adamu Abubakar Yarima, Likitan dabbobi a Jihar Kadunan Tarayyar Najeriya, ga kuma abinda yace,game da amsar wannan tambaya.

Dr Yarima: Gaskiyar maganar dai , Jemagu ba makafi ba ne, suna gani. To sai dai matsalar su Jemagu basa iya gani cikin duhu amma wadansu bangaren na Nau’in Jemagu, da dama daga cikin su idanuwan nasu kanana ne, ko kuma gashi yana rufe Idon.

Jemage yana tashi ne a cikin duhun dare ba tare da matsala ba kuma suna da tsarin tashi mai ban sha’awa. Shine abinda muke kira ‘Sonar system’, tsari ne wanda yake bambance abubuwan dake kewaye dasu ta hanyar karar kadawar sauti.

Saurayin mutum na iya jin sauti mai nisan kadawar sauti 20,000 a sakan daya. Jemage, ta wannan tsari na ‘Sonar system’ yana riskar nisan kadawar sauti kusan 50,000 da 20,000 a sakan daya. Tana aika wadannan saututtuka ne ta kowace fuska sau 20 ko 30 a sakan. Karfin jin sauti yana da karfin da jemage ba wai kawai zai fahimci kasancewar abu kusa dashi ba, amma yana gane inda abin yake da kadawarsa ko ta’ina.