1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsaro a tashoshin jiragen saman Turai

Umaru February 2, 2010

Kasashen Turai suna ci gaba da muhawara a kan hanyoyin tsaro a tashoshin jiragen saman su

https://p.dw.com/p/LpU8
Tashar jiragen saman birnin MunichHoto: cc-by-sa

Ko wace kasa ta kungiyar ita ce take da alhakin tsara yadda zata tafiyar da matakai na tsaro a tashoshin ta. Masana sun nuna cewar ana samun banbanci matuka tsakanin kasa da kasa a game dfa matakan na tsaro a tashoshin jiragen sama.

A tashar jiragen saman Schipol a Amsterdan tuni an fara amfani da na'urorin nan na binciken jikin dan Adam, wadanda ke iya gano makamai ko bama-bamai idan aka boye su a fatar jiki. To sai dai ya zuwa yanzu, sai fasinjan da yaso ne za'a yi masa binccike tare da wadnanan sabbin na'urori, saboda amfani dasu a yanzu din, gwaji ne kawai., tun da ministocin cikin gida na kungiyar hadin kan Turai sun kasa samun baki daya, a game da yadda za'a yi amfani da wadannan na'urori na bincike. HUkumarf kungiyar hadin kan TUrai ta bada shawarar amfani da na'urorin gaba daya a dukkanin tashoshin jiragen saman kasashen kungiyar, to amma kwamishinan shari'a ta kungiyar, Vivian Reding tayi gargadi a game da keta hakkin sirri na matafiya, tun da shike binciken zai kai har ga fatan jiki ne.

Tace bukatar mu ta tabbatar da tsaro ba zai sanya mu keta hakkin ko wane irin sirri na jama'a ba. Al'ummar mu ba kayaiyaki bane, amma mutane ne masu rai da numfashi.

Wasu yan majalisar Turai ma suna nuna shakkun su a game da wadannan na'urori na bincike. To amma duk da haka, gwmanatin Holland tana bukatar idan zai yiwu ta fara amfani da na'urorin na binciken jikn dan Adam cikin gaggawa. A Italiya, amn shirya fara amfani da wadannan na'urori a tashoshin jikragen sama biyu da suka fi girma, wato Fiumicino a Rome da Malpensa a Milan, ko da shike fasinjojin dake kan hanyar su zuwa Amerika da Israila kadai za'a yiwa bincike dasu. A Ingila, nan da yan kwanaki kalilan za'a fara amfani da na'urar a tashar jiragen sama ta Heathrow. FGaransa tace da farko tana son yin nazari kan wnanan na'ura ta bincike tukuna, inda ma za'a gudanar da bincike na gwaji kan wadanda suka yarda da hakan a birnin Paris. Wakilin musamman ta fuskar tsaro na kungiyar hadin kan Turai, Gilles de Kerchove yace bai kamata muhawarar da ake yi ta tsaya kan na'urorin binciken dan Adam kadai ba.

Yace Maganar da ake yi ta wuce ta na'urorti na fasaha a tashar jiragen sama. Wajibi ne a zabi zabi hanyoyi da dama da suka dace domin tabbatar da tsaron. Muna bukatar musayar labarai tsakanin hukumomin leken asiri da yan sanda. Wajibi ne mu rika sanin wadanne paspo ne aka sata wadanne irin Visa matafiya suke dasu.

Kerchove yace tsaro ba zai sau ta hanyar kara yawan fasaha kadai a tashoshi jiragen sama ba. Abin da yafi muhimmanci shine hade labaran da ake dasu wuri guda a kuma rika gagtgauta nazarin su. Ta wannan hanya da ya kamata a gano dan Nijeriyan nan da yayi kokarin fasa jirgin saman Delta Airlines raar Kirsimeti.

Kungiyar yan sanda a nan Jamus tayi suka ganin cewar a Jamus da kasashen Turai da dama, batun bincike a tashoshin jiragen sama, an kyale shi ne gaba daya a hannun kamfanoni masu zaman kansu. A halin yanzu, kungiyar hadin kan Turai ta kirkiro wata hukuma, wadda aka danka mata alhakin tabbatarda tsaro a tashoshin jiragen saman kasashen ta.

Mawallafi: Umaru Aliyu

Edita: Yahouza Sadissou