1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsaurara tsaro bayan harin kasuwa a Berlin

Ahmed Salisu
December 20, 2016

Tun bayan da babbar mota ta afka wa kasuwar Kirsimeti da ke babban birnin Jamus Berlin inda mutane 12 suka rasu yayin da wasu karin 48 suka jikkata an tsauraro tsaro.

https://p.dw.com/p/2Ub4n
Deutschland Berlin Sicherheitsmaßnahmen nach Anschlag
Hoto: Getty Images/M. Tantussi

Jami'an 'yan sanda a Jamus sun shiga farautar wani dan Tunusiya mai suna Anis Amri da ake zargi da hannunsa a harin da aka kai a kasuwar Kirsimeti a birnin Berlin, wanda Kungiyar IS ta yi ikirarin daukar nauyi.