1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsauraran dokokin mafaka a Sweden

Usman Shehu UsmanJune 22, 2016

'Yan majalisar dokokin kasar Sweden sun kada kuri'a da gagarumin rinjaye bisa tsaurara dokokin bada mafakar siyasa da kuma bada visa ga iyalan wadanda ke zama wajen kasar.

https://p.dw.com/p/1JB2Q
Schweden Stockholm Jagd auf Flüchtlinge Protest
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Ericsson

Kasar Sweden mai yawan mutane miliyan goma, a bara kadai ta karbi 'yan gudun hijira 163,000 abin da ke zama babban gwaji na karfin shigar da baki ga kasar, wace ke a yakin Skandanavian. Kudurin da aka amince da shi, ya dakatar da bada takardun zama na wushin gadi ga masu neman mafakar siyasa, kana an takaita yawan iyalan da za su samu visa don hadewa da 'yan gudun hijira 'yan uwansu, wadanda suka riga suka samu takardun zama cikin kasar ta Sweden. Kasar Sweden ita ce kasar da tafi dokoki masu sauki da ke bude kofa ga mafakar siya, kafin bara kasar ta fara daukar tsauraran matakai bisa 'yan gudun hijira da ke korara cikin kasar.

Sukar Jamus kan yara

Asusun kula da yara na MDD ya wallafa rahoto, inda ya soki halinda yara 'yan gudun hijira ke ciki a kasar Jamus. A cewar UNICEF, 'yan gudun hijira yara kanana, suna da kaskancin matsayin samun ilimi, idan aka kwatanta da takwarorinsu wadanda aka haifa a cikin kasar ta Jamus. Asusun ya kuma kara da cewa wani yanayi ne daban ake kula da yara 'yan gudun hijira, kan makomar basu izinin zama a kasar. Rahoton na UNICEF ya kara da cewa irin wannan bambancin da ake nuna wa yana kawo cikas na sajewar yaran da 'yan uwansu, a lokacin da suka fara zuwa makarantu bayan samun izinin zama. Kasar Jamus dai ita ce kan gaba wace 'yan gudun hijra ke neman shiga a fadin Turai.