Tsauraren matakan tsaro a Abuja
October 17, 2010A Najeriya jami'an tsaron sun tsaurara matakan tsaro a babban birnin ƙasar Abuja, bayan da ƙungiyar da takai harin ranar bikin samun 'yancin kan ƙasar, ta sake yin barazanar kai wani harin. Rohotonni sukace anga 'yan sanda masu kunce bama bamai, na bincikar ababen hawa musamman a kusa da filin jiragen sama dake Abuja, inda sai an binciki dukkan motar da za ta fita ko shiga filin jigin saman. Wani matafiyi a Abuja, yace shi kam bai taɓa ganin irin tsauraran matakan tsaro da aka ɗauka, kama daga jiya ba. A ranar Juma'a ne dai ƙungiya karen 'yan yankin Niger Delta wato MEND, ta ce za ta sake kai wasu hare-haren bama bamai, kamar waɗanda ta kai a Abuja ranar da aka yi bikin samun yancin kan ƙasar na shekaru 50.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu