1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsawaita takunkumin dokar Trump kan baki

Gazali Abdou Tasawa
March 30, 2017

A kasar Amirka, alkalin babbar kotun jihar Hawai Derrick Watson ya sake tsawaita matakin takunkumin da ya saka wa dokar nan da Shugaba Donald Trump ya dauka kan baki da 'yan gudun hijira.

https://p.dw.com/p/2aHuv
Derrick Watson
Hoto: picture-alliance/AP Photo/G. F. Lee

Derrick Watson ya kuma bayyana cewa zai mayar da wannan mataki nasa daga na wucan gadi zuwa na har abada. 

Kuma baban antoni janar na kotun jihar ta Hawai ya sanar da cewa matakin da alkali Derrick Watson ya dauka a halin yanzu, mataki ne da a idon doka na iya haramta wa gwamnatin Donald Trump gudanar da duk wata kwaskwarima ga dokar  ta baki da 'yan gudun hijira. 

Makonni biyu da suka gabata ne dai alkalin babbar kotun jihar ta hawai Derrick Watson ya dauki mataki saka takunkumi ga wannan doka ta Shugaba Trump wacce ta tanadi haramta wa 'yan asalin wasu kasashe shida akasarinsu na Musulmi shiga kasar ta Amirka.