1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsiyayar mai a gaɓar tekun Mexiko

June 17, 2010

Kamfanin BP ya ware wani asusun biyan diyya na dala miliyan dubu 20

https://p.dw.com/p/NsoE
Shugabanni da wasu wakilan BP da suka gana da Obama a fadar White HouseHoto: AP

A dangane da malalar man fetir dake ci-gaba da addabar gaɓar tekun Mexiko kamfanin haƙan mai na Birtaniya wato BP ya ware asusun dala miliyan dubu 20 don biyan diyya ga waɗanda matsalar malalar man ta shafa. Bayan ya gana da shugabannin kamfani na BP a birnin Washington shugaban Amirka Barak Obama ya ce wata hukuma mai zaman kanta za ta kula da asusun. Kamfanin na BP kuma ya ce a watannin da suka saura a wannan shekara ba zai ba da riba ga masu hanayen jari a cikinsa ba. Shugaban BP Carl-Henric Svanberg ya faɗawa manema labarai a Washington cewa ya yi nadama ga bala'in na tsiyayar mai.

"Ina son in yi amfani da wannan damar domin in nemi gafarar ga al'ummar Amirka a madadin dukkan ma'aikatan BP, waɗanda ɗaukacinsu ke zaune a gaɓar tekun Amirka. Ina gode muku ga haƙurin da kuka nuna a wannan mawuyacin lokaci."

A wani lokaci yau ɗin babban shugaban zartaswa BP Tony Hayward zai bayyana gaban wani kwamitin majalisun dokokin Amirka domin amsa tambayoyi masu tsauri.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Umaru Aliyu