1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon shugaban ƙasar Ghana ya ƙaryata zargin da ake yi masa na shirya juyin mulki.

October 26, 2006
https://p.dw.com/p/BueO

Tsohon shugaban ƙasar Ghana, Jerry Rawlings, ya ƙaryata zargin da shugaba mai ci yanzu, John Kuffour, ke yi masa na shirya wani sabon juyin mulki a ƙasar. Da yake fira da maneman labarai yau a birnin Accra, bayan dawowarsa daga wata ziyarar da ya kai a ƙetare, Jerry Rawlings ya ce halin shugaba Kuffour ne ya dinga yaɗa ƙarya a ko’ina, don jan hankullan jama’an ƙasar daga taɓargazar cin hanci da rashawa da addabar gwamnatinsa.

Shi dai Rawlings, wanda ya shafe kusan shekaru 20 yana mulkin ƙasar ta Ghana, ya ƙalubalanci shugaba Kuffour da ya fito fili ya ba da hujjar zargin da yake yi masa, na cewa ya tafi wata ƙasa mai arzikin man fetur ne, don neman taimakon kuɗaɗen da zai shirya juyin mulkin da su.

Shugaba John Kuffour dai ya zargi Rawling ɗin ne a wani kamfen, na yaƙin neman zaɓen cike gurbin kujerar majalisa a ƙarshen makon da ya gabata, amma bai ba da ƙarin haske ga zargin ba.

A cikin ’yan watannin da suka wuce dai, an yi ta samun jami’an gwamnatin Kuffour ɗin cikin taɓargaza daban-daban na cin hanci da rashawa. Hakan ne ma ya tilasa wa wani ministansa yin murabus saboda wasu maƙudan kuɗaɗen da aka ce ya bai wa farkarsa. Kazalika kuma an ɗaukaka ƙarar wasu manyan jami’an ’yan sandan ƙasar, game da laifufukan da ke da jiɓinta da safarar miyagun ƙwayoyi, bayan ɓacewar wani kayan cocain da jami’an tsaro ke sa ido a kansa.