1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon shugaban kasar Haiti Jean Bertrand Ristide ya bukaci komawa gida

February 23, 2006
https://p.dw.com/p/Bv7A

Sabon zaɓaɓɓen shugaban kasar Haiti rene Preval yace tsarin mulkin kasar ya baiwa tsohon shugaban kasar Jean Bertrand Aristide na da ikon komowa gida idan har yana bukatar yin hakan. A wata hira da ya yi da manema labarai Preval yace kundin tsarin mulkin ya fayyace filla filla cewa babu wani dan kasar da ke bukatar Visa domin fita ko kuma shiga kasar sa ta haihuwa, a saboda haka yace tsohon shugaban na da ikon komowa gida. Aristide ya bar kasar Haitin ne a cikin watan Fabrairu na shekara ta 2004 bayan matsanancin bore ga gwamnatin sa da kuma tashe tashen hankula a kasar. Majalisar dinkin duniya ta tura dubban jamián kiyaye zaman lafiya domin domin tabbatar da doka da oda.

Tsohon shugaban kasar Jean Bertrand Aristide yace zai yi shawara da sabon zabbaben shugaban kasar tare da majalisar dinkin duniya da kuma wasu kasashe domin tsaida ranar da zai komo gida.