1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta nemi sanin matsayin Trump kan siyasar ketare

Salissou Boukari
November 11, 2016

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande ya sanar a wannan Juma'a cewa, abin da suke jira da sabon shugaban Amirka da aka zaba Donald Trump, shi ne samun haske kan tsarin siyasarsa ta harkokin ketare.

https://p.dw.com/p/2SYmR
Paris | Treffen der Verteidigungsminister der Anti-IS-Koalition in Paris - Francois Hollande
Hoto: picture-alliance/dpa/C. Platiau

Shugaban na Faransa ya ce daga cikin abubuwan da suke son karin hasken a cikinsa, akwai musamman ma abun da ya shafi harkokin tsaro, da kuma matakin sojan da kasashen ke dauka kan Siriya da Iraki a yakin da ake da 'yan kungiyar IS.

Shugaban na Faransa ya kuma kara da cewa, suna bukatar sanin matsayin na Donald Trump kan batun yarjejeniyar da aka cimma kan dumamanar yanayi a birnin Paris, wanda Trump din ya sha alwashin canza wa fasali a lokacin yana yakin neman zabe, kuma Shugaba Hollande ya ci gaba da cewa:

"Zaben Donald Trump a matsayin shugaban Amirka, ya tilasta wa kasashen Turai su kasance masu nuna matsayi guda na gaskiya, ta yadda za su iya fusakantar kalubalen da ke a gaban su. Sannan kuma za mu samu damar tantance yadda hulda za ta kasance tsakanin Tarayyar Turai da Amirka tare da sabin hukumomin na Amirka, kuma wannan shine tunani na dukannin kasashe membobin kungiyar Tarayyar Turai."